Acts 11

Bitrus Ya Bayyana Abubuwan da Ya Yi

1Manzanni da ʼyanʼuwa koʼina a Yahudiya suka ji cewa Alʼummai ma sun karɓi maganar Allah. 2Saboda haka saʼad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi 3suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.”

4Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa: 5“Ina a birnin Yoffa ina adduʼa, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake. 6Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namomin jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama. 7Saʼan nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’

8“Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’

9“Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’ 10Wannan ya faru har sau uku, saʼan nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama.

11“Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake. 12Ruhu ya ce mini kada in yi wata wata game da tafiya tare da su. Waɗannan ʼyanʼuwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin. 13Ya kuma gaya mana yadda wani malaʼika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. 14Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’

15“Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko. 16Saʼan nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce: ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 17To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”

18Saʼad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To fa, har Alʼummai ma Allah ya da tuba zuwa rai.”

Ikkilisiya a Antiyok

19To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai. 20Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Helenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu. 21Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

22Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok. 23Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu. 24Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.

25Saʼan nan Barnabas ya tafi Tarsus don ya nemi Shawul, 26saʼad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawul suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.

27A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima. 28Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za ta bazu a dukan duniyar Romawa. (Wannan kuwa ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.) 29Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudunmawa ga ʼyanʼuwan da suke zama a Yahudiya. 30Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawul.

Copyright information for HauSRK